A yau ake kammala shirin raba abincin buda baki da tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya dauki nauyi a karkashin gidauniyarsa ta Abubakar Bukola Saraki Foundation.
Shirin ciyarwar, wanda aka gudanar da shi a jihohin arewa guda biyar da suka hada da Sokoto da Kogi da Niger da mahaifarsa jihar Kwara da kuma babban birnin tarayya Abuja an fara shi ne daga ranar 15 ga watan Ramadana kuma za a kammala a yau.
Dr. Abubakar Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar Kwara sau biyu, kuma tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar nan daga shekara ta 2015 zuwa 2019 ya kasance yana irin wannan aikin alherin a cikin kowane wata na Ramadan karkashin gidauniyarsa
Dubunnan mutane ne dai suke amfana daga rabon abincin wanda ake yi a masallatai da gidajen gyaran hali da sauran wuraren da mabukata ke zuwa domin buɗa baki bayan an sha ruwa.
Gidauniyar Abubakar Bukola Saraki dai ta daɗe tana irin wannan aikin na taimakawa mabuƙata a lokuta da dama kuma a wannan shekarar ma an ɗauki nauyin ciyarwa ne domin ragewa al’umma wahalhalun da suke sha musamman wajen samun abinda za su ci a yayin da al’ummar kasar nan ke ci gaba da shan wahala sakamakon tashin kayan abinci da ragowar kayan masarufi.
