Kungiyar kwallon kafa ta Barau Football Academy, za ta fafata a gasar cin kofin gidauniyar Rochas Foundation Football ta shekarar 2023 da za a yi a Abuja.
Independent Mirror ta rawaito cewa kungiyar ta Barau Football Academy, da ke nan Kano, na daga cikin kungiyoyi 10 da zasu barje gomi a gasar.
A wata wasika da gidauniyar ta Rochas Foundation ta fitar a wannan makon, ta ce gasar ta kwanaki hudu an shirya tane domin wakilai wato [Agents] su samu damar ganin yan wasan da zasu iya dauka domin fitar da su kasashen waje.
Sanarwar ta kara da cewa ana saran wakilai wato [Agents] din daga kasashen Ingila da Holland ne zasu halarci gasar don ganewa idanuwansu matasan yan wasan Najeriya.
Shugaban kungiyar ta Barau Football Academy, Ibrahim Shitu Chanji, ya ce tuni kungiyarsa tayi shiri namusamman, domin wakilci mai inganci a gasar ta kwanaki hudu da zata gudana.
Akalla kungiyoyi Goma ne dai zasu fafata a gasar da zata gudana a filin wasa Moshood Abiola da ke birnin tarayya Abuja.
Kungiyoyi Goman sun hada da Rochas Foundation Football Club, Football Clubs, Sunzeal Football Club, IB Sporting Dream, Yaba FC.
Sauran sune Inspiration Sports Academy, Barau Football Academy Kano, Kwara Footbal Academy, PRO Line FC, One Touch Unit Star FC.
Bayan kammala wasannin gasar kuma, ana sanar masu sanya ido kan yan wasan, zasu samu damar ganawa da yan wasan da aka zaba a ranar Litinin 6 ga Nuwamba domin sanin irin tagomashin da suka samu.
Wasannin gasar an tsara gudanar da su kamar haka…..
ROCHAS FOUNDATION FOOTBALL CLUB VS SUNZEAL FOOTBALL CLUB
TIME: 10:30PM-12:15PM
DATE: 2ND NOVEMBER, 2023
YABA FC VS INSPIRATION SPORTS ACADEMY
TIME: 12:15PM-1:25PM
DATE: 2ND NOVEMBER, 2023
BARAU ACADEMY VS KWARA FOOTBALL ACADEMY (K.F.A)
TIME: 1:25PM-2:30PM
DATE: 2ND NOVEMBER, 2023
PRO LINE FC VS IB SPORTING DREAM
TIME: 10:30PM-12:15PM
DATE: 3RD NOVEMBER, 2023
ONE TOUCH VS UNIT STAR FC
TIME: 12:15PM-1:25PM
DATE: 3RD NOVEMBER, 2023
SUNZEAL FOOTBALL CLUB VS KWARA FOOTBALL ACADEMY(K.F.A)
TIME: 1:25PM-2:30PM
DATE: 3RD NOVEMBER, 2023
ROCHAS FOUNDATION FOOTBALL CLUB VS PRO LINE FC
TIME: 10:30PM-12:15PM
DATE: 4TH
NOVEMBER, 2023
BARAU ACADEMY VS INSPIRATION SPORTS ACADEMY
TIME: 12:15PM-1:25PM
DATE: 4TH
NOVEMBER, 2023
KWARA FOOTBALL ACADEMY (K.F.A) VS ONE TOUCH
TIME: 1:25PM-2:30PM
DATE: 4TH
NOVEMBER, 2023
YABA FC VS INSPIRATION FOOTBALL CLUB
TIME: 10:30PM-12:15PM
DATE: 5TH
NOVEMBER, 2023
UNIT STAR FC VS BARAU ACADEMY
TIME: 12:15PM-1:25PM
DATE: 5TH
NOVEMBER, 2023
IB SPORTING DREAM VS SUNZEAL FOOTBALL CLUB
TIME: 12:15PM-1:25PM
DATE: 5TH
NOVEMBER, 2023
