Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya biya kudin aikin da za a yiwa matashinnan Abdurraba dan karamar hukumar Ungogo da ya samu lalura wanda fuskarsa ta kunbura.
Independent Mirror ta ruwaito Shugaban ma’aikatan Ofishin Sanata Barau Farfesa Muhammad Bin Abdallah ne ya jagoranci biyan kudin aikin Sama Da Naira Miliyan daya ga matashin a wannan Rana ta Alhamis 23 ga Nuwambar 2023.
Muhammad Bin Abdallah ya ce Sanata Barau ya biya kudinne sakamakon yadda matshin ke tsananin bukatar kulawa, baya ga yadda matashin ke kokarin neman na kansa.
Matashi Abdurraba dai ya gamu da wani ciwo da kawo yanzu haka fuskarsa ta kunbura kuma ciwo na damunsa, da ta kai baya iya komi yana zaune a gida.
Amma dai likitoci a Asibitin Malam Aminu Kano sunce, ba za a yiwa matashin aikin ba, sai zuwa fuskarsa ta sace.
Tuni ake ci gaba da mika sakon jaje da kuma mika sakon alhinin abin da ya faru ga matashin wanda a baya dalibi ne da ya kammala jama’ia.
Itama Mahaifiyar matashi Abdurraba ta bayyana farin cikin wannan tallafin kudin da aka biya dan nata, duk da cewa dama suna cikin wani hali.
Ta kuma sake nuna farin cikinta ga duk wanda suka tallafawa dan nata bisa wannan hali da ya tsinci kansa a ciki.
