Home FeaturesMai Sharar Titi Da Aka Kade A Murnar Cin Zaben Gwamnan Kano Abba Gida-Gida Na cikin Mawuyacin Hali

Mai Sharar Titi Da Aka Kade A Murnar Cin Zaben Gwamnan Kano Abba Gida-Gida Na cikin Mawuyacin Hali

by Ahmad Hamisu Gwale

Wata Dattijuwa Mai Suna Hussaina Muhammad na rokon Al’umma su kawo mata dauki domin ceto rayuwarta daga karayar da take fama da ita.

Dattijiwar da ke zaune a unguwar Sani Mainagge a yankin Karamar hukumar Gwale, ta ce ta samu ibtailin raunin a lokacin da take aikin ta na sharar Titi sai wasu mutane suka Kade ta saboda suna Murnar Cin Zaben Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida).

A zantawarta da Sashen Hausa na Independent Mirror ta ce a ranar 29 ga Mayun shekarar da muke ciki (2023) da aka kade ta take cikin Mawuyacin Hali lamarin da yasa take neman temakon alummar jihar Kano da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf kasancewarsa mai tausayin talakawa.

“Tin a lokacin da abin ya faru wasu sunyi kokarin kai ni Asibiti domin likitoci su kula da ni, amma har zuwa yanzu raunin bai warke ba.” a cewarta.

Ta kuma ce san da abin ya faru wanda ya yi mata raunin ya tsere, ba ta re da ya tsaya domin ya duba halin da ta tsinci kanta ba.

Haka Zalika Hajiya Hussaini na bukatar Al’umma da kuma gwamnatoci a kowanne mataki da su kawo Mata dauki don ceto rayuwarta.

Ta kuma bukaci Jama’a da su dubi halin da ta shiga na rashin babu, da kuma rashin abin da za taci da take Fama da shi.

Don taimakawa Dattijiwa Hussaini Muhammad Za a iya kira wannan number din 0701 719 9364 domin samun karin bayani.

Ko ga masu taimkawa a iya tura abin da ya samu a wannan Bank….

Acct: 0440361937

Gt Bank

Ali Ahmad Hamisu.

 

Allah ya sa a dace.

Related Articles

Leave a Comment