Binciken da wasu Kungiyoyi 17 suka gudanar a jihar Kano dake Arewa maso yammacin Nigeria ya tabbatar da cewa shirin bunkasa ilimin Mata (Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment AGILE) ba shi da Alaka ta kusa ko ta nesa da Yahudawa ko kuma bata addinin musulunci ko Al’adar mutanen jihar.
Independent Mirror Ta ruwaito Binciken na kungiyoyin na zuwa ne bayan wata jita-jita da ake yadawa cewa shirin wai asalinsa Yahudawa ne suke daukar nauyi don bata tarbiyya da Addinin musulunci da mutanen Kano wanda bayan waccar jita-jita kungiyoyin suka gudanar da bincike suka kuma gano akasin hakan.
Rahoton binciken da kungiyoyin sukayi wanda Ambasada Nura Abdullahi Sarki wanda ke a matsayin Sakatare gamayyar kungiyoyin ya sanyawa hanu ya ce bayan bibiyar shugabannin shirin da dalilan da suke amfanar Shirin da iyayen yara da gwamnatin jihar Kano da dukkan masu ruwa da tsaki ya gano cewa duk zarge-zargen da ake yi bashi da tushe ballatana makama.
Rahoton ya kuma bukaci alummar jihar Kano da suyi watsi da wadancan zarge-zarge wanda a cewa rahoton Kage ne kawai, har ma ya bukaci dukkan wani mutum ko rukuni da yake da ra’ayin gudanar da wani binciken yana iya yi kuma a shirye suke su taimaka masa wajen gudanar da binciken.
Ga cikakken rahoton binciken:
GAMAYYAR KUNGIYOYIN MATASAN MASU RADIN KARE JIHAR KANO.
Sakamakon wata sanarwa da wasu daidaiku ke yi game da shirin nan na AGILE a Jihar Kano.
Gamayyar kungiyoyi Sunbi diddigi tare da tuntubar wadanda abin ya shafe, musamman Gwamnati da jami’an shirin, da wasu daga cikin iyayen yaran sama da 800,000 dake makarantun Gwamnati a Jihar Kano, da su kansu daliban, da malaman da ke ba da horon, da sauran masu ruwa da tsaki, Haka kuma mun bibiyi ita kanta manhajar da ake horar da yaran, tare da sauran manhajojin sauran darussan sakandire. Ba mu sami wani dalili da za a ce ta sa ba wa Addini da al’adu da kuma zamantakewarmu, amma bamu samu ba.
Don haka wannan batu kage ne mara tushe da muka kasa gane abinda masu yada shi ke burin cimma, sabanin cigaban al’ummar Jihar Kano baki daya.
A zurfafa bincikenmu, mun tabbatar cewa Gwamnatin Jihar Kano ta fara gudanar da shirin AGILE tun shekarar 2021, tare da jihohin Borno, Katsina, Kaduna, Kebbi, Plateau da Ekiti.
Kuma saboda alfanin shirin a yanzu haka wasu karin jihohi sun sami nasarar shiga. Kamar Jigawa, Zamfara, Bauchi, Gombe, Yobe, Kogi, Niger, Kwara da sauransu.
Rawar da Bankin Duniya ke takawa kawai ita ce shine ya ba da lamanin kudaden gudanarwa, wanda kurna za a biya cikin wasu shekaru nan gaba.
Mun bincika kuma mun tabbatar shirin AGILE ba shi da wata alaka ta kusa ko ta nesa da Yahudawaba kamar yadda zuzuta hakan , a Fili ko a boye. Kuma dukkan al’umma suna ganin irin alfanun da wannan shiri ya kawo a makarantun sakandire na duk fadin Jihar Kano.
Wannan kungiya tamu tana kira ga dukkan jama’a da su bibiyi makarantun ya nkunansu, iyaye kuma su tuntubi ‘ya’yayensu, do min tabbatar da sahihiyar gaskiya r lamarin.
Kofar jami’an wannan shiri, da ta mahukunta a bude take ko da yaushe, ga masu neman karin bayani, ko shawara, ko tattaunawa game da dukkan tsare-tsaren wannan shiri, a ofishinsu da ke hawa na uku, Gidan Murtala, Kofar Nassarawa, ci kin Birnin Kano.
Muna shawartar al’umma da muguji yada jita -jita ba tare da bincike a kan ingancin labarurrukan yanar gizo ba, musamman game da muhimmin kokari da Ma’aikatar Ilmi key iwajen inganta rayuwar al’umma domin ci gaban Jihar Kano baki daya.
