Ministin Ilimi Farfesa Tahir Mamman SAN, ya kaddamar da kwamitin shirin bunkasa Ilimin Mata na Adolescent Girls Initiative For Learning and Empowering AGILE a fadin kasar nan.
Independent Mirror ta ruwaito Kaddamar da kwamitin shirin na AGILE ya gudana a makon nan a ofishin ministan da ke birnin tarayya Abuja.
Shirin bunkasa Ilimin Mata na Adolescent Girls Initiative For Learning and Empowering AGILEa Najeriya na samun tallafin bankin Duniya.
Cikin wadanda suka halarci kaddamar da kwamitin shirin na AGILE, sun hada da Ministin Ilimi Farfesa Tahir Mamman SAN, da karamin ministan na Ilimi Dr Yusuf Sununu.
Sauran sun hada da Ministir Matasa Dakta Jamila Bio da kuma Daraktan Bankin Duniya a Najeriya da Sakataren UBEC na kasa.
Haka zalika Kwamishinonin Ilimi da wakilan shirin na AGILE na Jihohin kasar nan 18 da sauran masu ruwa da ki a kasar nan, duka suna daga cikin wadanda suka halarci taron.
A jawabinsa Ministin Ilimi Farfesa Tahir Mamman ya bayyana Gwamnatin Najeriya za ta bawa shirin goyan baya yadda ya kamata domin ciyar da ilimin Mata gaba.
Shi kuwa Shubham Chaudhuri, Daraktan Bankin Duniya a Najeriya ya ce bankin burinsa shi ne ci gaba da tallafawa kasashe masu tasowa.
Mista Steve Ohaeri wanda ya wakilci ministan kudi ya ce samuwar shirin na AGILE a Najeriya zai sake farfado da ilimin Mata da kuma kanan Yara.
Ana saran kwamitin da Ministan na Ilimi Tahir Mamman ya kaddamar, zai kawo rahotan aikin da aka bashi a Shekarar 2024
