Home UncategorizedAthletic Football Kaduna ta lashe gasar Yan kasa da shekara 13 ta Bundesliga Cup

Athletic Football Kaduna ta lashe gasar Yan kasa da shekara 13 ta Bundesliga Cup

by Ahmad Hamisu Gwale

Kungiyar kwallon kafa ta Athletic Football Academy Kaduna ta doke Kuso Boys Football Academy Kaduna da ci 3-0 a wasan karshe a karshen mako.

Wasan wanda aka shirya tsakanin Matasa ‘Yan kasa da shekara 13 na Kofin Bundesliga Kaduna wato (Under-13 Bundesliga Cup Kaduna )

Kungiyoyin Matasa 24 ne suka shiga gasar wadda aka fara a watan Augustan shekara ta 2023, kuma wasan ya ja hankalin masoya kwallon kafa da dama a Kaduna.

Tsofaffin ‘yan wasa da suka buga gasar Premier Najeriya da kuma wasu a wajen kasar nan ne suka halarci wasan na karshen da ya gudana a filin wasa na Secret Heart da ke barakin ‘yan sanda a jihar Kaduna.

Jim kadan bayan tashi daga wasan dai baki da dama ne suka mika kyaututtakan da aka lashe a wasan karshen.

Inda Kungiyar Athletic ta samu Babban kofi kuma dan wasan ta Yassir Awwal ya fi zura kwallo a gasar inda ya jefa kwallaye 7 kuma mafi kwazo a gasar.

Haka zalika ya samu kyautar takalmi da kwallo na zinare, sai kuma kungiyar Kuso Boys Football Academy ta samu kyautar karamin kofi bayan zama ta biyu a gasar.

Kawowa yanzu tagomashin Gasar Bundesliga ta kasar Jamus na bunkasa a nan Kaduna da ma arewacin Najeriya.

Musamman ganin yadda irin wadannan gasa ke jawowa gasar farin jini a tsakanin Matasa, Kuma gasar ta Bundesliga na kara yin fice.

Mohammed Mohammed wakilin tashar DW Hausa a Kaduna, Kuma Jakadan Bundesliga wanda ya shirya gasar ya ce wannan ba shi ne na farko da aka fara shirya Gasar ba.

Inda ya kara da cewa gasar cin kofin Bundesliga a a Kaduna, musamman ta wannan lokaci itace gasa ta farko na Matasa ‘Yan kasa da shekara 13 da aka gudanar.

Muhammad ya kuma ce ”’Na kwashe shekara 5 ina shirya wannan gasa, sai dai mun yi tunanin farawa ta Yara wanda hakan zai karawa Yara kwarin gwiwa, da kuma jawo hankalin su akan wannan gasa ta Bundesliga da ake bugawa a kasar Jamus’’,

Muhammad ya ci gaba da cewa ‘’Gaskiya ya ji dadin yadda matasan suka taka rawa a gasar kuma abin ya birge kowa da kowa sai dai kuma akwai bukatar Hukumar da ke shirya gasar Bundesliga wato DFL da kuma ita kanta Bundesliga da ke kasar Jamus su bada ta su gudummawar domin gasar ta fi haka’’,

‘’Kuma hakan zai karawa Bundesliga suna a Kaduna da manyan birane irin su Kano da arewacin Najeriya baki daya’’,

Ya kuma karkare da cewa nan bada jimawa ba za a fara shirye-shiryen sake yin wata gasar a cikin shekara ta 2024, kuma ana sa ran gasar za ta yi armashi sosai.

Related Articles

Leave a Comment